MATAIMAKIN SHUGABAN KASAR BURUNDI YA ZIYARCI WASU WURARE NA JAMI'A

 

  A jiya Laraba, bayan kammala taron bude bikin jami'a wanda ya gudana a dakin taro na Alhaji Muh'd Indimi dake cikin tsdangayar Ma'adanai, mai girma mataimakin shugaban Burundi ya ziyarci sassa daban daban na jami'ar Afrikiyya. Mai girma shugaban jami’a Prof. Kamal Muh'd Ubaid shine wanda ya jagorance shi izuwa wuraren, sun fara da dakunan jarabawa na yanar gizo, sannan suka ziyarci wasu daga cikin tsangayun jami'ar, daga nan kuma suka leka dakunan watsa labarai na Talabijin da Rediyo,inda har aka gudanar da fira da bakon.