MATAIMAKIN SHUGABAN KASAR SUDAN DARE DA TAKWARANSA NA KASAR BURUNDI SUN HALARCI TARON JAMI'A

 A jiya Laraba 09/01/2019 aka fara gudanar da taron jami'a wanda ta saba shiryawa akowace shekara, taron wanda yake tattaro mahukuntar jami'ar daga kasashe daban daban. Mai girma mataimakin shugaban kasar Sudan Dr. Usman Muh'd Yusuf Kabar da takwaranshi na kasar Burundi Mr. Gaston Sandimo sun halarci taron wanda ya gudana a dakin taro na Alhaji Muh'd Indimi dake tsangayar Ma'adanai. Daukacin mahukuntar jami'ar tun daga malamai, shuwagabannin tsangayu, shuwagabannin dalibai, da sauran ma'aikata duk sun halarci taron. Mai girma shugaban jami'a Prof. Kamal Muh'd Ubaid yayi maraba ga daukacin mahalarta taron, sannan yayi jawabin tsare tsaren jami'a akan kasashen Afrika wanda cibiyar Musulinci dake cikin jami'ar ta Afrikiyya ta soma a 1988. Har ila yau mai girma shugaban jami'ar yayi jinjina gami da addu'a ga wanda suka fara wannan aikin. taron dai ya tattauna kan abubuwa da dama kamar yadda aka saba a duk shekara. Ministar ilimi ta kasar Burundi ta tofa albarkacin bakinta, inda ta kara tabbatar da kula alakar ilimi tsakanin kasashen biyu, ministar ta yabi jami'a wajen kokarin sauya tunanin yen Afrika da tunkudasu izuwa fagen neman ilimi da aiki da shi.