MINISTAR ILIMI MAI ZURFI TA KARBI SHAWARWARIN KWAMITIN DAIDAITA AL`AMURAN JAMI`AR KASA DA KSA TA AFRIKA

A yau Laraba ne da Azhar 2/9/2020, mai girma ministar ilimi mai zurfi da binkicen kimiyya farfesa Intisar Az-Zain Sageerun  ta karbi bakuncin kwamitin daidaita al`amuran jami`ar kasa da kasa ta Afrika, wanda aka kafa shi bisa jagorancin farfesa Yusuf Mukhtar Al-Ameen tsohon shugaban jami`a, - shugaban kwamiti- taron ya hadar da wakilan ma`aikatar ilimi mai zurfi da binkicen kimiyya da kuma sauran yan kwamitin.

A farkon taron mai girma ministar ta yi maraba da yan kwamitin, tana mai mika godiya gare su bisa irin namijin kokarin da suka yi lokacin gudanar da aikin kwamitin da kuma karbar nawin da aka dora musu na wannan aikin.

Bayan wannan jawabin nata ne sai farfesa Yusuf Mukhtar Al-Ameen shugaban kwamitin ya dora da nasa jawabin inda ya godewa mai girma ministar bisa yardarta da kuma zabin da ta yi ga yan wannan kwamiti, wadanda suka yi aiki kwarai da gaske da ya kamata a jinjina musu, wanda a karshe suka fitar da shawarwarin da zasu taimaka wajen sabunta dokoki da tsarukan jami`ar, da kuma ciyar da su gaba ta hanyar kowane matakanta, babba daga ciki shine sabunta yarjejeniya ta musamman da jami`ar Afrika da kuma tsarukanta na asali, ban da ka`idojin tsara kwamitin amintattu, sannan ya tabbatar da jin dadin sa na abubuwan da aka tattauna masu amfani a lokacin zaman ayyukan kwamitin, kamar yadda ya tabbatar da jin dadinsa da irin shawarwarin da aka fitar wadanda zasu taimaka a cikin masalahar jaami`a da kuma manufarta.

Wannan kenan, a karshen jawabin sa a kuma wani irin lokaci na tarihi mai girma tsohon shugaban jami`a ya mika mika wasu wasikoki masu mahimmacin da wasu shawarwari ga mai girma minister, kuma wakiliya ta yarjejeniyar musamman da jami`ar kasa da kasa ta Afrika a sabon tsarinta da salonta, wanda ya aminta da jami`ar da kuma sakonta da manufofinta da kuma tsarin asali na jami`ar sannan da ka`idojin tsara kwamitin amintattun jami`a.

A nata jawabin a taron mai girma minister ta yaba da irin kokarin da da wannan kwamitin ya yi tsawon lokacin aikin sa, tana mai nuni da cewa sun damu da dorewar cigaban jami`a da kuma sabon gudunmawarta da suke gani gaba daya a nan Sudan da kuma wajenta, sannan ta yaba da irin shawarwarin da kwamitin ya fitar wanda abun alfahari ne ga Sudan da ma`aikatar da kuma jami`a kamar dai yadda ta fada, sannan ta bayyana cewa jami`a tana taka rawa mai mahimmanci sosai akan sha`anin dibulomasiyyar kasashe ta hanyar tsofaffin dalibanta da suka watsu a cikin sassan duniya, a karshen jawabinta mai girma ministar ta tabbatarwa da kwamitin kwadayinta da bibiyarta akan ganin an zartar da wadannan shawarwarin kafin zaman kwamitin amintattun jami`a a nan kusa.

Wannan kenan, dukkan mahalarta taron sun aminta da jami`a da sakonta da manufofinta da kuma irin rawar daa take takawa wajen yada ilimi, sannan sun nuna kwadayin su bisa cigaban dorewar jami`ar, sannan kuma sun bada shawarwari masu yawa.