MATAIMAKIN SHUGABAN JAMI`A TA FANNIN KUDI DA GUDANARWA YA GANA DA SHUWAGABANNIN KWALEJOJI, TARON KUMA YA AMINCE DA CIGABA DA KARATU A RANAR ASHIRIN DA WANNAN WATAN DA MUKE CIKI

A safiyar yau Lahadi ne 6/9/2020, Farfesa Abdul-Azeem Al-Muhal, Mataimakin shugaban jami`a ta fannin kudi da gudanarwa, ya jagoranci wani taron wanda ya hadar da shugabannin kwalejoji, daraktocin cibiyoyi da shugabannin bangarori daban-daban na ilimi a jami’ar, a dakin taro na Farfesa Ad-Dayyib Zainul-Abideen da ke cikin jami’ar, inda taron ya tattauna kan matsaloli da kalubalen da ke gaban jami’ar a wannan lokaci.

A farkon taron, Farfesa Al-Muhal ya yi maraba da mahalarta taron, yana mai nuni da cewa makasudin taron shi ne yin tunani game da shirye-shiryen da ake yi na komawa karatu a jami'ar da duk abin da ke da nasaba da tsarin koyo da koyarwa dangane da daukan matakai na wurwuri na shirya muhallin koyo da koyarwar daidai da dokoki da ka'idojin kiwon lafiya da ake bi. Kamar yadda taron ya tabbatar da bukatar cigaba da harkar koyo da koyarwa a jami'ar da kuma hada kai da yin aiki tare kamar yadda ya dace. Taron ya fito da shawarwari da dama, mafi mahimmanci daga cikinsu shine tabbatar da cigaba da karatu a fannoni daban-daban na jami'ar a ranar 9/20/2020. Kamar yadda taron ya ba da umarnin cigaba da kwamitin dakunan da suka gabata. Kamar yadda mahalarta taron kuma suka aminta a bisa wajibcin yin jigilar ma'aikata daga inda suke zuwa jami'ar bisa rukunin su mabambanta, sannan da kuma wajibcin shirya zaman majalisar ilimi ta jami`a da wuri-wuri don zartar da sakamakon jarrabawa. A wannan gurin ne, mahalarta taron suka ba da shawarar cewa ya kamata mataimakin shugaban jami`a a fannin kudi da gudanarwa Farfesa Al-Muhal, ya hada gwiwa da ma'aikatar Ilimi mai zurfi da binkicen kimiyya, don daidaita yanayin harkar gudanarwa a jami'ar. Kamar yadda taron ya aminta kan wajibcin shirya zaman kmamitocin kolejoji bisa tsari don tattaunawa da amincewa da shirye-shirye daban-daban, amma a bayar da fifikon bayar da kudade a harkar koyo da koyarwa a mataki mai zuwa.