MAI GIRMA MATAIMAKIN SHUGABAN JAMI`A TA FANNIN KUDI DA GUDANARWA YA GANA DA MA`AIKATAN JAMI`A KUMA YA KIRAYE SU AKAN HADA KARFI DA KARFE DA ZAMA TSINTSIYA MADAURINKI DAYA

A safiyar yau lahadi ne 31/8/2020 a dakin taro na Afrika dake jami`a, mai girma mataimakin shugaban jami`a ta fannin kudi da gudanarwa Farfesa Abdul-Azeem Al-Muheel ya gana da ma`aikatan jami`a, ganawar dake cike da nuna kauna da kishin jami`a. A cikin jawabin nasa mai girma mataimakin shugaban jami`a ya yi nuni akan cewa jami`a zata iya tsallake wannan irin yanayin da take tafiya a cikin sa, domin ta taba kasancewa a kwatankwacin irin wannan yanayi a tarihinta mai tsawo, kuma ta fita daga cikin sa tare da kara samun karfin gwiwa da daidaituwar al`amura, yana mai nuni zuwa ga cewa yanayin jami`ar ya sha bamban dana sauran  jami`o`I, saboda kasancewarta tana da yarjejeniyar hedikwata tare da hukumar Sudan da kuma wasu yarjejeniyar alakar kasa da kasa tare da wasu bangarori da dama.

A gefe guda kuma Farfesa Al-Muheel ya tabbatar da cewa kwamitin daidaita al`amuran jami`a wanda ma`aikatar ilimi mai zurfi ta kafa, ya gama fitar da rahotannin sa da shawarwarin san a karshe, kuma zasu mika su zuwa ga ma`aikatar ilimi mai zurfi da binkicen kimiyya a cikin kwanaki biyu masu zuwa.

Sannan kuma mai girma mataimakin shugaban jami`a ya gabatar da wani Karin haske akan halin da jami` a take ciki game da sha`anin kudi a tsakankanin lokacin da ya huce, ta hanyar wasu alkaluma da ya ambata wadanda suke nuni da cewa jami`a tana fama wasu nauye-nauye da basuka da suka yi mata nawi a kafadarta, in da ya bayyana cewa ya dauki wasu matakai da dama don farfado da bangaren kudi, hakan ya kasance ne ta hanyar sanya wani kasafin ciki gibi daga 15/8/2020 har zuwa 31/12/2020, sannan kuma da sanya kwamitin da zasu tsara kasafin shekarar 2021 tare da kula da abubuwa da dama da ka iya zuwa su dawo. Tare da jaddada cewa harkar koyo da koyarwa utace mafi kyawun abunda za a ribata, sannan kuma ya ja hankalin ma`aikatan jami`a kan wajabcin nisantar gurguzu da sa`insa a tsakanin su kamar yadda ya fada.

Sannan ya bayyana cewa za a zartar da kalandar karatun jami`a kamar yadda take, kuma za a fara karatu kamar yadda aka sa, sannan kuma yana mai yin bushara da cewa za a warware dukkan wadannan matsaloli na kudi kadan-kadan a hankali daidai da yadda tsare-tsare suke da yardar Allah ta`alah, yana mai kara kira ga daukacin ma`aikatan jami`a akan hada karfi da karfe gu guda da kuma zama tsintsiya madauri daya.