MAI GIRMA SHUGABAN JAMI`A YA MIKA TAKARDAR YIN MURABUS DAGA GUDANAR DA HUKUMAR JAMI`A

 

Mai girma shugaban jami`a Farfesa Yusuf Mukhtar Al-Ameen ya mika takardar neman yin murabus dinsa daga gudanar da jami`a ga mai girma ministar ilimi mai zurfi da binkicen kimiyya, yana mai danganta yin murabus din nasa  da irin yanayin da jami`ar take tafiya a cikin sa, wanda hakan ba zai iya bashi damar gudanar da ita ba kamar yadda ya fada.

Sannan mai girma ministar ilimi mai zurfi da binkicen kimiyya ta fitar da doka data hukunta karbar yin murabus din mai girma shugaban jami`a , sannan kuma ta umarci bangarorin da abun ya shafa da sanya dokar a inda za a zartar da ita.