BIYAN ALBASHIN WATA GUDA GA MA`AIKATA DA LEBURORIN JAMI`A A MATSAYIN KYAUTA DAGA JAMI`A

Dr Ja`afar Hassan Muhammad mataimakin shugaban jami`a a fannin kudi da gudanarwa ya fitar da dokar da ta hukunta bada albashin wata guda kyauta ga ma`aikata da leburorin jami`a, hakan ya kasance ne biyo bayan ganawar da aka yi tsakanin hukumar jami`a da kuma wakilan ma`aikata da leburori na jami`a, wanda a cikinta ma`aikatan da kuma leburorin suka nemi hakan daga hukumar jami`a.