CIGABA DA YIN RIJISTAR KAKAR KARATUN ZANGO NA BIYU HAR ZUWA RANAR ALHAMIS MAI ZUWA

Ofishin karbar dalibai da yi musu rijista yana kara sanar da cewa ana cigaba da yin rijistar kakar karatun zango na biyu Maris/Yuli, a ofishin karbar dalibai da yi musu rijista har zuwa ranar Alhamis mai zuwa 19 ga watan Maris ga dukkanin kwalejoji, ya zama dole ga daliban da busu sami damar yin rijista ba da su hanzarta don karasa ayyukan yin rijistar su. wannan sanarwar tana matsayin dama ta karshe don yin rijista, ba za a duba wani roko ba na yin rijista bayan wannan lokacin.