JAMI`A TA FITAR DA HUKUNCIN DAKATAR DA KARATU DA JARRABOBI NA TSAWON WATA GUDA

A yau Lahadi ne 15 ga watan Maris 2020, farfesa Yusuf Mukhtar Al-Ameen shugaban jami`a ya fitar da dokar dakatar da karatu a dukkan sasannin jami`a da kuma rufe jami`ar na tsawon wata daya daga yanzu, dogara akan hukuncin da hukumar Sudan ta fitar na rufe jami`o`I na tsawon wata guda, don daukan matakan kariya dana kiwon lafiya a kasar.

Kamar yadda hukuncin kuma ya nusantar da wadannan abubuwan masu zuwa:

1- Jingine dukkan wasu ayyuka da hana taruwa guri daya a jami`a har zuwa lokacin da za a sake samun wata sanarwar.

2- Takaice lokutan shirye-shiryen da`awah a masallatan jami`a guda 3 da kuma nisantar cikowa.

3- Cigaba da ayyukan yau da kullum ga ma`aikatan jami`a har zuwa lokacin da za a sake samun wata sanarwar.

4- Ya zama dole akan kwamitin karta-kwana a kullum ya dinga bibiyar halin lafiyar dalibai da ma`aikata a jami`a, da kuma mika rahoto akai-akai.

Wannan dokar ta hada da dakatar da zana jarrabobi su ma.