HUKUMAR JAMI`A TA ZAUNA TARO DA SHUWAGABANNIN KWALEJOJI DA DARAKTOCIN CIBIYOYI NA JAMI`A

A safiyar yau laraba 12/2/2020, a dakin taro na Ad-dayyib Zainul-Abideen dake ginin hukumar jami`a, aka zauna taron shuwagabannin kwalejojin jami`a da daraktocin cibiyoyi da ofisoshi, a karkashin jagorancin farfesa Musa Daha Tayallah mataimakin shugaban jami`a ta fannin ilimi da al`ada, a inda taron ya tabo abubuwa da yawa da suka ta `allaka ga cigaban jami`ar da tabbatuwarta.

A farkon taron mai girma mataimakin shugaba ya gabatar da karin haske akan halin da jami`a take ciki, da kuma hanyoyin da hukumar jami`ar ta bi a tsawon wannan al`Amari da ya faru, yana nuni I zuwa cewa jami`a tana tafiya a yanayi mai kyau da kwanciyar hankali, yana mai bushara da sakin albashin malaman jami`a masu karantarwa cikin kwanaki biyun nan masu zuwa da kudin cikin gida (junai din Sudan) kamar yadda shirye-shirye suna gudana na sakin albashin wata biyu da kudin kasar waje (dala) a yan kwanakin nan masu zuwa, kamar yadda za a saki sauran albashin watannin da kudin cikin gida (junai din Sudan), sannan ya nutsantar da kowa cewa hukumar jami`a tare da taimakon ofishin kula da al`amuran dalibai sun samu damar samar da kayan abincin dalibai na tsawon watanni shida, sannan ya roki farfesa Sayyid Hamid Huraiz da ya karbi nauwin tafi da hukumar jami`ar, kamar yadda ya roki ma`aikatan jami`a akan wajabcin hadin kai da taimakon juna da daukar nauwi dai-dai da aikin kowa  a gun aikinsa, yana mai tabbatar da cewa kawayen jami`ar masu kwadayin dorewar jami`ar ne da kuma sakonta, kamar yadda ya tabbatar da kokarin kasar wacce ministar ma`aikatar ilimi mai zurfi farfesa Intisar Azzain Saagirun take wakilta akan dorewar jami`ar da kuma sakonta.

Shima a nasa bangaren farfesa Sayyid Hamid Huraiz wanda aka dorawa nauwin shugaban jami`a ya tabbatar da neman hanzarinsa ga ma`aikatar ilimi mai zurfi akan karbar nauwin tafiyar da al`amuran hukumar jami`ar, yana mai bada hanzari ga abokan aikinsa malamai akan kin amsa kiran sun a karbar nauwin tafiyar da al`amuran hukumar jami`a, yana mai nuni da cewa yardar da ma`aikata suke da ita ga jami`a, it ace mafi girma daga kowace irin yarda da zasu bashi daga kowane bangare ta kasance, sannan yace tun lokacin da ya zo jami`a bai samu komai daga gareta ba sai alkhairi.

Wannan kenan, wadanda suka taru a wannan taron sun aminta abusa wajabcin kiyaye sakon jami`a da martabarta, suna masu tabbatar da kokarin su mai girma wajen fitar da jami`a zuwa gaba.