KUNGIYAR TSOFAFFIN DALIBAN JAMI`A TA FITAR DA WANI BAYANI: WANDA A CIKIN SA TAKE MUSANTA ZARGIN TSOFAFFIN DALIBAN JAMI`A DA TA`ADDANCI

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai

 

Bayanin Ofishin zartarwa na kungiyar tsofaffin daliban Jami'ar kasa da kasa ta Afirka akan zargin jami’ar na kyankyashe ‘yan ta’adda

 

Allah madaukakin sarki yana fada a cikin littafinsa mai hikima:

Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fasiki ya zo muku da wani labara, to ku tabbatar don kada ku afkawa mutane abisa  jahilci sai ku wayi gari kuna masu nadama abusa hakan (aya ta 6)

 

Bayan haka:

kungiyar tsofaffin daliban Jami'ar kasa da kasa ta Afirka ta kasance tana bibiyar da yawa daga abubuwan da ake yadawa akan jami`ar na kyankyashi yan ta`adda kuma ta bibiyi martanin ɗalibanta a cikin kasar hedkwatar jami`ar wato (sudan) da kuma wajen ƙasar, saboda haka muke bayanin waɗannan abubuwa:

 

1 / Tun bayan kafuwar Cibiyar Musulunci ta Afirka a shekarar 1966, dalibai sun kasance suna karatu a cikinta da tsari na tsakiya madaidaici (ma`ana babu sakwo-sakwo babu zurfafawa kuma), wadan yake da nufin gina al'umma mai lumana da aminci wanda ya wofanta daga bangaranci da tsatstsauran ra'ayi.

2 / Bayan da Cibiyar Musulunci ta bunkasa zuwa Jami'ar kasa da kasa ta Afrika, wanda a yanzu take da kwalejoji 22, da kuma cibiyoyi da ma`ahad a fannoni daban-daban na ilimin kimiyya da adabi, an cigaba da tafiya a cikin tsarin tsaka-tsaki, wanda ya sanya kasashen Afirka da yawa turo yaransu zuwa Sudan, musamman Jami'ar kasa da kasa ta Afirka don cigaba da karatun jami'a. Jami`a ta fitar da dalibai masu yawa wanda adadinsu ya wuce 37,000 maza da mata,  wadanda suka bazu cikin kasashe 90, mafi yawansu a Afirka da Asiya suna dauke da sakon jami’ar da kyawawan manufofinta wadanda ke neman kawo cigaban al’umma.

3 / Har kawo yanzu bai  tabbata an samu ba, a dogon tarihin jami'ar cewa ana tuhumar wani daya daga cikin tsofaffin dalibanta a kowace kasa da laifin ta`addanci ko bangaranci ko wani abu da ya taba zaman lafiyar mutane ko kuma sauran ayyukan da suke barazana da ga al`umar dan adam, bari ma dai mun ga sabanin haka, alal misali, tsofaffin daliban jami'a sun sami lambobin yabo na girmamawa daga Shugabancin Jamhuriyar kasar Burkina Faso don amincewa da rawar da tsofaffin daliban jami'a suka taka gun bunkasa al'umar yankin a Burkina Faso.

4 / Irin wadannan maganganun da basu dace ba, ba kawai iya tsofaffin daliban jami`a suke cutarwa ba, suna cutar da har ma jami’ar da kuma hedkwatar kasar ta Sudan.

5 / tare da kakkausan harshe kungiya tana sukan waɗannan zarge-zargen na karya, waɗanda ba su da tushe.

6 / Kungiya tana tabbatar da cewa zata cigaba da kare martabar jami’ar da kuma tsofaffin dalibanta,  kuma za su dauki matakan da suka dace na doka kan duk mutumin da ransa ta sa shi yada irin wadannan bayanan na karya.

 

Allah yana nan a bayan nufi, kuma shi ne yake shiryarwa zuwa ga hanya.

 

Ofishin Zartarwa na Kungiyar tsofaffin daliban Jami`ar kasa da kasa ta Afrika