JAMI`A TANA NEMAN LADA GUN ALLAH NA JURE RASHIN SHEIKH ABDUR-RAHMAN ALU-SHEIKH

Allah ya yiwa Sheikh Abdur-Rahman Alu-Sheikh rasuwa, memba na kwamitin Amintattun Jami'ar Kasa da Kasa ta Afrika daga Masarautar Saudiyya, kuma daya daga cikin masu tallafa mata da dalibanta, inda da yawa daga cikin 'yan Afirka suka shiga maraici kuma baƙin ciki ya lullube su, abusa mutumin da cuta, ko tsufa, ko kuma aiki busu hana shi biyan bukatun musulmai ba a Afirka da lokacinsa, da kuɗinsa da kuma tunaninsa. Sheikh Abdur-Rahman Alu-Sheikh ya kasance mutum ne mai himma wanda bai san kasala ba, kuma muyum ne mai azama wanda bai san rauni ba. Ya kasance yana haduwa da mu a gidansa a cikin mawuyacin hali na rashin lafiya mutu fakwai-rai fakwai yana jagorantar majalisa, yana kula da komai kuma yana neman ƙaramin bayani sosai akan abubuwa. Ba ya tuna da damuwar gaba daya kuma baya bada amsa akan yanayin sa da lafiyarsa ba, face karin yabo da godiya ga Allah.Ya yi iya kokarin sa kuma na kasance ina fadawa ’yan’uwa lokacin da ya kasance bako a kasarmu a halin na rashin lafiya matsananci ,da kuma magana da Farfesa Kamal Muhammad Obaid. wallahi Sheikh bai bar uzuri ga wani mai neman uzuri ba.

Mai girma Alu-Shekh, Allah ya yi masa rahama, ya gina zaure a cibiyar dalibai mata a jami'a da sunan malamar Da`awah ta Amurkan nan Aminatu As-Salami domin tunawa da ita a koda yaushe, kamar yadda ya gina hade da kara tsayin gungun kwalejojon koyon aikin jiya da kuma koyon gwaje-gwajen likitanci a jami`a.

Allah ya yi masa rahama ya karbe shi a cikin  salihai. Muna yiwa kan mu  ta'aziyya sannan muna yiwa danginsa, da masoyansa, da dalibansa a duk faɗin duniya, kuma daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma.