MINISTAR ILIMI MAI ZURFI: JAMI`AR KASA DA KASA TA AFRIKA ABAR ALFAHARI CE GA KASAR SUDAN KUMA TANA MATSAYIN DIFLOMASIYYA TA ILIMI DA KUMA KASA

Ministar Ilimi mai zurfi: Jami'ar Kasa da Kasa ta Afirka abar alfahari ce ga kasar Sudan kuma tana matsayin diflomasiya ta ilimi da kuma kasa.

Ministan Ilimi mai zurfi: Jami'a wata jan layi ce da ba zamu yarda a soketa ba, ko a soki saƙonta.

Ministan Babban Ilimi: Mun karyata bayanin wasu bangarori na siffanta jami'ar a matsayin wurin haifar da ta'addanci.

Ministar Ilimi mai zurfi: sannan jami'ar tana ba da gudummawa matuka gun musayar wayewa da al'adu tsakanin mutane.

Ministar Ilimi mai zurfi: Gwamnatin kasar Sudan tana da sha'awar cigaban jami'ar da cigaban aikinta na musulinci madaidaici.

Ministar Ilimi mai zurfi: Babu wani tsari a cikin gwamnati na soke yarjejeniyar hedkwatar.

Ministar Ilimi mai zurfi: muna yabawa da rawar da jami’ar ke takawa wajen ilimantar da ‘ya’yan musulmai da sauran yayan nahiyar Afirka.

Ministar Ilimi mai zurfi: Jami'ar Kasa da Kasa ta Afirka ita ce mafi mahimmancin jami'a a Sudan a gurin mu.