MAJALISAR JAMI`A TA ZAUNA TARONTA KARKASHIN JAGORANCIN MINISTAR ILIMI MAI ZURFI, KUMA MAJALISAR TA AMINCE DA MURABUS DIN FARFESA KAMAL UBAID

A yau Laraba da Azuhur, 5 ga watan Fabrairu 2020, aka zauna taron majalisar Jami’a a ma’aikatar Ilimi mai zurfi da binkicen kimiyya, karkashin jagorancin farfesa Intisar Az-zain Sagirun, Ministan Ilimi mai zurfi da binkicen Kimiyya, tare da halartar membobin majalisar daga ciki da wajen jami’ar. A inda majalisar ta amince da yin murabus din farfesa Kamal Muhammad Ubaid daga shugabancin jami`ar, abusa cewa ministar zata nada sabon shugaba da zai jagoranci tafiyar da aikin jami’ar har zuwa lokacin da kwamitin Amintattu na jami’ar zai zauna nan bada dadewa ba.

 

A jawabinta gabanin taron, Ministar Ilimi mai zurfi ta tabbatar da mahimmancin jami'ar ga Sudan, tare da nuna cewa abar alfahari ce ga Sudan kuma tana matsayin diflomasiya ta ilimi da da ta kasa ga Sudan, sannan ta ce jami'ar ta jan layi ce da ba zasu yarda a soketa ba, ko a soki saƙonta ba, tana mai jaddada ƙin yardarta ga wasu ɓangarorin da suke siffanta jami'ar a matsayin tushen haifar da ta'addanci, tare da nuna cewa jami`ar tana ba da gudummawa sosai wajen musayar wayewar kai da al'adu tsakanin mutane, sannan mai girma ministar ta jaddada kokarin gwamnatin Sudan kan cigaban jami'ar da cigaban aikinta na musulinci madaidaici, sannan mai girma minista ta yanke cewa  gwamnati bata da nufin soke yarjejeniyar hedkwatar. Sannan kuma ta yabi rawar da jami'ar ke da shi wajen ilmantar da yayan musulmai da sauran mutane na nahiyar Afirka, kuma ta fada da babban baki cewa jami`ar kasa da kasa ta Afrika ita ce mafi muhimmanci jami'a a Sudan a gurin su, kuma ta tabbatar da zasu taimakawa dangantakar jami'ar ta waje za kuma a fadada ta.

 

A nasa bangaren, farfesa Kamal Muhammad Ubaid, shugaban jami`a, ya mika godiyarsa mai yawa ga Ma’aikatar Ilimi mai zurfi da kuma mai girma Minista saboda fahimtarta da kuma kai-kawonta tare da cigaban al’amuran da ke faruwa a jami’ar, tare da jaddada goyon bayansa mara iyaka ga sabuwar gwamnati daga duk sanda aka gabatar da sh, yana kuma mai bda shawara da a zauna taron kwamitin amintattu na Jami’ar nan bada dadewa ba, sannan ya kuma ba da shawarar kafa wata tawaga wacce ministar harkokin Ilimi mai zurfi zata jagoranta tare da sabon shugaban jami`a, da tsohon shugaban jami’a, don su ziyarci membobin kwamitin amintattu na jami’ar a kasashensu tare da ba su tabbacin cigaban jami’ar a kan hanyarta mai kyau, mai girma Ministar ta nuna gamsuwarta da wannan kudurin, a inda  za a tsara hakan nan gaba.