MA`AIKATAN JAMI`A DA DALIBANTA SUN JADDADA RASHIN YARDAR SU DA MURABUS DIN SHUGABAN JAMI`AR KASA DA KASA TA AFRICA

Ma’aikata a Jami’ar Kasa da Kasa ta Africa da dalibanta sun jaddada cikakken rashin yardarm su da murabus din Farfesa Kamal Mohamed Obeid, shugabar jami’ar kuma wanda farfado da cigabanta, yayin da ma’aikatan jami’ar tare da bangarorinsu daban-daban suka cigaba da kaikawon su tsakanin gine-ginen hukumar jami’ar da gidan shugaban inda suka nemansa da ya janye hukuncinsa da yayi na murabus tare da barin shugabancin jami’ar a cikin irin wannan yanayi, suna neman da ya cigaba da yunƙurin da ya sanya jami’ar kasancewa a cikin jerin sauran jami`o`i da suka cigaba a duniya.

Ma’aikatan jami’ar sun shirya babban taro a jiya, Lahadi, inda suka hadu akan mai girma shugaban jami’ar ya cigaba da kasancewa a matsayin shugaba har zuwa karshen wa`adinsa a watan Afrilu 2021.

A tuna kuma cewa tsofaffin daliban jami’ar wanda suka watsu a cikin kasashe sama da tamanin (80) sun ta tuntubar jami’ar suna bukatar lallai mai girma Farfesa Kamal Muhammad Obaid ya cigaba da gudanarwa da shugabancin jami’ar da kuma cigaba da bunkasa jami`ar kamar yadda ya shirya a lokacin shugabancinsa.