JAMI`A TA FITAR DA KARIN BAYANI

 

 

 

 

 

 

Jami'ar Kasa da Kasa ta Afirka ta maida martini kan tuhumar wani memban Kwamitin yaki da yiwa dukiyar kasa zagon kasa

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai

Jami'ar Kasa da Kasa ta Afirka

Karin bayani na (3)

Kun san cewa jami’ar ta ba da wasu bayanai guda biyu ga ra’ayoyin jama’a kan wasu batutuwa da maganganu a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, jami’ar ta isu da iya bayanai biyun da suka gabata, amma mun samu kanmu ta yadda ya zama dole mu fitar da wani karin haske game da bayanan da wani memba na Kwamitin yaki da yiwa dukiyar kasa zagon kasa, yayin da ya bayyanawa kafafen yada labarai cewa ( mafi girman tallafi ga wata ma’aikatar ilimi a kasar ya kasance na Jami'ar Kasa da Kasa ne, wanda yakai junai miliyan (400) a kowace shekara daga Ma'aikatar Kudi) saboda hakane jami'ar, don ta kare kanta da hakkokinta  ta fitar da bayyanai kamar haka:

Na farko: Gwamnatin Sudan, kamar sauran kasashe ce a cikin wannan ma`aikata, kasancewarta memba a cikin kwamitin amintattu yasa take cika alkawuranta ga jami'ar tun daga tsakiyar shekarun saba'in wato (1970) a matsayin albashi yayin da yake shiga asusun jami'a yadda ya dace cikin tsari.

Na biyu: Adadin kudin da jami’ar ta karba, wanda gwamnatin Sudan ta bada izini a cikin kasafin kudin shekara ta 2019 (junai miliyan 50 ne) kawai ba biliyan ba. Inda ake fitar da junai miliyan (4,1) na Sudan kowane wata, kuma kudin yana zuwa ne ta hanyar Ma'aikatar Ilimi mafi zurfi da Nazarin Ilimin Kimiyya, kuma ana sanya shi a asusun jami'a a Bankin Sudan ba (biliyan ɗari huɗu ba ne).

Na uku: An ba da izinin bada ne wannan kudin a taron haɗin gwiwa na Majalisar Jami'ar da Kwamitin Kudi, wanda membobinsu sune Ministan Kudi, Gwamnan Babban Bankin Sudan, Sakataren Ofishin zakka, sai wakili daga ma`aikatar Ilimi mai zurfi, da sauransu.

Na hudu: Adadin wannan kudi na miliyan (4.1) na junai din Sudan idan aka auna shi da jimillar abun da ake biyan albashin ma’aikatan jami’a da kudin gida wato (junai din Sudan) ya yi daidai da kashi 40% kawai, yayin da idan aka tara albashin da ake biyan ma’aikata na kudin cikin gida da na waje, ba zai wuce kashi 4% ba, A sani cewa albarkatun jami’ar na kashin kanta suna ba da kashi 77% na kasafin kudin aikin jami`a, wanda albashin Ma'aikata da take biya bai taka kara ya karya ba daga ciki.

Irin waɗannan maganganun da ba a tabbatar da su ba suna muzanta sunan jami'a da gaskiyarta a gun masu taimakamata, sunan da ya cika duniya, don haka ya kamata a tantance wannan bayanan da kuma kididdiga ingantacciya kafin a fade su kuma su zama mallaka ga kafofin watsa labarai.

Na biyar: Dangane da bita: tsarin asali na jami'a a babi na hudu (hukunce – hukuncin samar da kudade da gyara tsarin asali) yana nuni a cikin kasafin kudi da bita sakin layi mai zuwa:

Tsarin doka na 30 (1) Jami'ar za ta kasance tana da kasafin kuɗi na shekara-shekara mai cin gashin kansa wanda ke ƙididdige kudaden shiga da kuɗaɗen da zata kasha, sannan kuma yana ƙarƙashin kulawa da aiwatarwa kamar yadda aka tsara a cikin ƙa'idodin tsarin kuɗi da tsarin lissafi.

30 (2) Kwamitin Amintattu zai sanya mai bincike na doka don duba asusun jami'ar bisa ga ka'idodin da kwamitin Amintattu ya kafa.

A cikin amincewa da tsarin asali da gyarashi,, yana nuni i zuwa:

Tsarin doka na 33 (3) Ba za a iya gyara tsarin asali ba sai da hukuncin  da kwamitin Amintarwa ya gabatar da mafi yawan kashi biyu na ɓangarorin mambobinsu waɗanda ke halartan taron a dokance.

Na shida: Akwai fatwa wacce Babban mataimaki na hedkwatar ya bayar na rashin cancantar ware Babban Darakta Janar na duba asusun jami’ar bisa tanade-tanaden doka da yarjejeniyar hedikwatar, kuma wannan fatwa akwaita a cikin files din jami’ar, dana Babban mataimakin kasa, dana Majalisa dana kuma ma’aikatar Harkokin Wajen.

Na bakwai: Jami'ar tana da cikakken haƙƙin ɗaukar dukkan matakan shari'a da suka wajaba don kiyaye martabarta da mutuncin ta.

 

Ofishin hulda da Jama'a da yada labarai