MA`AIKATAN JAMI`AR KASA DA KASA TA AFRICA SUN YI WATSI DA MURABUS DIN SHUGABAN JAMI`AR FARFESA KAMAL UBAID

A wani matsayi na tarihi game da tarihin Jami’ar kasa da kasa ta Afirka, ma’aikatan jami’a,da malamai, sun  yi watsi da murabus din da Farfesa Kamal Mohamed Obaid, shugaban jami’ar ya gabatar, bayan jinkirta taron  kwamitin amintattun jami`a  karo na (26), kamar yadda majalisar Zartarwa na Kasa ya bada umarni, wanda aka tsara zai gudana a ranar 9 da ranar 10 ga wannan watan da muke ciki. ma’aikatan sun hadu a wani babban taron da suka shirya a safiyar yau Lahadi, 12 ga watan Janairu, 2020 a cibiyar taruka na Afirka, a gaban Farfesa Kamal Obeid, shugaban jami’ar, gaba daya sun amince da yin watsi da murabus din da shugaban ya gabatar har zuwa lokacin kammala wa`adinsa. Wanda zai ƙare a watan Afrilu 2021.

 

A nasa jawabin a gaban taron, shugaban jami’ar ya bayyanawa ma’aikatan duk irin matakan da jami’ar ta dauka a lokutan da suka gabata da kuma ganawarta da shugaban kasa da kuma Ministan ilimi mai zurfi da dukkan bangarori na hedikwatar kasar, don bayani akan dabi`ar  jami’ar da tsarinta, ta yaba da cikakken hadin gwiwar da jami’ar ta samu daga dukkanin wadannan hukumomin, musamman fadar Shugaban rikon kwaryar kasar da ministan ilimi ,ai zurfi da binciken  kimiyya, don fahimtarsu game da sakon jami'a da yanayinsa, da kuma samar musu da dukkan abubuwanda suke nema don gudanar da  taron Kwamitin Amintattu na jami'ar. Mau girma shugaban jami`a yace don kwadayin  jami'ar na kiyaye martabar kasar da ikonta, jami`a ta yanke shawara nan da nan na amimcewa da hukuncin majalisar zartarwa na daga taron kwamitin amintattu, ya kara da cewa jami'ar tana biyaya da dokoki da hukunce-hukuncen hedkwatar kasar ta Sudan, yana mai tabbatar da kudirinsa na cigaba da kokarinsa na tallafawa jami’ar ta hanyar yin duk abin da zai iya don daukaka jami’ar da kuma kiyaye sakon ta, sannan yace yana matukar farin ciki cewa yana da ‘ya’ya 40,000 a Afirka, ma`ana tsofaffin daliban jami`a, Wadanda suka kammala karatun jami’ar wandanda suka  bazu ko'ina a cikin duniya. sannan kuma ya shawarci ma’aikatan jami’ar kan bukatar hada hannu tare, da kuma yin watsi da rabe-rabe a tsakaninsu, don kiyaye jami’ar da dalibanta wadanda ke matsayin jakadun  Sudan a kasashensu.

 

Bayan haka a yayin taron, da yawa daga cikin ma’aikatan jami’ar da shugabanninta, maza da mata sun yi Magana, inda suka bayyana kuma suka hadu gaba dayansu akan  tabbatuwar  Farfesa Kamal Muhammad Obaid a matsayin shugaban jami’ar, don tsallakawa da jami’ar zuwa gaba, tare da bayyana nasarori da babban cigaba da jami’ar ta shaida lokacin mulkinsa.