KUNGIYAR LIKITOCI TA DALIBAN AFRICA TA GUDANAR DA TARONTA NA LAFIYA NA 7

A ranakun Juma’a da Asabar ne, aka gudanar da taron lafiya na kungiyar likitoci ta daliban Afirka a dakin taro na Afirka da ke jami’a, inda bikin bude taron ya samu karramawar halartar mai girma Farfesa Kamal Muhammad Obaid shugaban Jami’ar, da Dr. Umar Al-Adil, shugaban  Kwalejin Kiwon Lafiya kuma mai kula da kungiyar, da wasu dalibai da dama, da likitoci, da ma’aikata a fannin likitanci daga ciki da wajen jami’ar. Inda Shugaban Jami’ar a cikin jawabin da ya gabatar agun bude taron kungiyar ya tabbatar da kokarin kungiyar sosai ta hanyar cigabanta da kuma shirye-shiryen da suke gabatarwa da suka shafi matsalolin kiwon lafiya a Afirka, yana mai tabbatar da cewa jami’ar zata cigaba da tallafawa kungiyar da kuma tsayawa tare da ita a dukkan ayyukanta da shirye-shiryenta.

An cigaba da gudanar da zaman tattaunawar a jiya da ranar Asabar, yayin da aka kammala taron a yammacin yau Asabar tare da halartar mutane da dama, wanda hakan yake tabbatar da nasarar taron da kuma kyakkyawan tsari.