AN KAMMALA TARON "SHIRIYOYIN ALLAH A CIKIN ALQUR`ANI MAI GIRMA

A Jiya Jumma'a ne da rana, 10 ga watan Janairu 2020, a dakin taro na Indimi dake Jami'ar, aka kamala tare da rufe taron kasa da kasa kan SHIRIYOYIN ALLAH A CIKIN ALKUR’ANI MAI GIRMA wanda KUJERAR SHIRIYOYIN ALLAH A CIKIN AL-QUR’ANI MAI GIRMA a Jami’ar Ummul Qurah da ke Makkatul Mukarramah ta shirya tare da hadin gwiwar Kwalejin Alqur`ani mai girma na cikin Jami’a, wanda ya kwashe tsawon kwanaki biyu. A inda bikin rufe taron ya samu karramawa ta halartar shugaban jami`a Farfesa Kamal Muhammad Obaid, da Farfesa Yahya Al-Zamzami Shugaban kujerar shiriyoyin allah a cikin Al-qur’ani mai girma a Jami’ar Ummul Qurah, da kuma wasu masu bincike da mahalarta taron daga mabambamtan kasashe.

A jawabin da ya gabatar a gurin rufe taron, mai girma shugaban jami’a ya godewa dukkan mahalarta da baƙin jami’ar, tare da jaddada cewa yin taron a jami’ar abin alfahari ne gareta, musamman ganin yadda yake magana game da alqur’ani mai girma wanda dama shine abun da jami’ar da ɗalibanta suka fi bawa mahimmanci.

A nasa bangaren, Farfesa Yahya Al-Zamzami, Shugaban shirin KUJERAR SHIRIYOYIN ALLAH A CIKIN AL-QUR’ANI MAI GIRMA ya godewa Jami’ar, da malamanta, da kuma Dalibanta, saboda kyakkyawar karbar bakunci da kuma tsari mai kyau, tare da tabbatar da cigaban alaka da hadin gwiwa tsakanin cibiyoyin guda biyu gurin hidimtawa littafin Allah madaukakin sarki.

A karshen taron, Dr Yassin Qary ya karanto shawarwarin da taron ya fitar, manya daga cikinsu sune:

Shirya wasu bincike a fagen girmama Allah Madaukakin Sarki da shirya wasu shirye-shirye na ilimi, da na kafofin yada labarai da kuma na tarbiyya akan girmama Allah Madaukakin Sarki.

Kafa hadin gwiwar duniya don samar da shirye-shirye na aikace akan girmama Allah Madaukakin Sarki.

Kamar yadda Sakatariyar taron ta karrama wasu bangarorin da suka taimaka gun nasarar taron.