AN FARA TARON SHIRIYOYIN ALLAH A CIKIN ALQUR`ANI MAI GIRMA

A safiyar yau Alhamis ne 9 ga watan Junairu 2020, aka fara gudanar da shirin "SHIRIYOYIN Allah a cikin Alqur’ani mai girma" wanda Kwalejin Alqur’ani mai girma a jami’ar ta shirya tare da hadin gwiwar “KUJERAR SHIRIYOYIN ALQUR`ANI” ta Jami’ar Ummul Qurah da ke Makkatul Mukarramah, bisa girmamawar jakadan Khadimul Haramaini  mai girma malam Aliy Hassan Ja`afar, da kuma mai girma shugaban jami`a farfesa Kamal Muhammad Ubaid, da kuma farfesa Yahya Al-Zamzami Shugaban shirin “KUJERAR SHIRIYOYIN ALQUR`ANI” a jami’ar Ummul Qurah da ke Makkatul Mukarramah da gungun masana da masu bincike daga sassan duniya.

A yayin bude taron, shugaban jami’ar ya yi jawabin maraba ga baki wadanda suka halarci taron, tare da mika godiyarsa ga jami’ar Ummul Qurah, wacce ta baiwa jami’ar karramawar yin hidima ga alqur’ani, wanda ya nuna cewa jami’ar tsawon tarihinta ta kasance cikin hidimar Littafin Allah Madaukakin Sarki.

Shi ma a nasa bangaren, Farfesa Yahya Al-Zamzami, Shugaban shirin “KUJERAR SHIRIYOYIN ALQUR`ANI” na Jami’ar Makkatul Mukarramah, ya godewa jami’ar da kwamitin shirya taron saboda cikakken hadin kai da kyakkyawan tsari, tare da bada tabbacin cigaba da hadin gwiwa tsakanin jami’o’in biyu a cikin hidimtawa addinin Musulunci da Musulmai.