Wasu mahimman darasi da za a yi la'akari a lokacin watan Ramadan acikin da Jami'ar kasa da kasa ta Afrika.

\

 

Daga: Abdel-Badea Hamza

 

Kafin watan Ramadan, Jami'ar kasa da kasa ta Afrika tana da masallatai daban-daban suna shirye don karɓar wannan wata mai alfarma, inda wadannan masallatai suke dauke da hasken lantarki suna suna kasha ido, kuma masallatai suna cike da masu bautawa Allah ba dare ba rana, sannan kuma jama`ane ke fitowa daga ko'ina cikin duniya suna haduwa domin karfafa alaka da kuma hadin kai tsakanin al'ummar musulmi wanda yake kawo amincewa da kai, jin kai kai a tsakanin musulmai.

Kowace shekara, masallatan jami'a suna haske da fitilun dmasu kayatar wa don shirye-shiryen wannan wata mai albarka, ruhin mumini tana samun nutsuwa, kuma sukan rungumi juna a cikin bangaskiya, girmamawa ga Karin tsoron Allah tare da karatun Alkur'ani mai girma da wasu karatutukan addini da ke haifar da zaman lafiya, jinkai da kwanciyar hankali ga al`umma a cikin masallaci a kowane bangare.

wannan jami'a ta bambanta da sauran jami`oi ta hanyar fice da tayi bangaren al'adu da kuma bambancin kabilu a cikin mafi kyawun tsari wanda hakan yana daga cikin muhimman abubuwa a Musulunci wato hadin kai.

   Kowace shekara, idan watan Ramadan yazo, kungiyoyi, cibiyoyi da kungiyoyin agaji sburin suga sun samu  damar isa ga daliban jami'a a domin wanda ya canza rayukan su da kuma inganta dabi'u da jin kai,. Allah ya karbi ibadunmu.

 Allah Madaukakin Sarki Ya wadatar da mu alherin dake cikin wannan wata kuma ya amintar damu.