Kwamitin kafa Bankin Afrika sun Gudanar Da mitin a ofishin Shugaban Jami`a.

A ranar Lahadi 12 ga watan mayu, Farfesa Kamal Mohamed Obeid, Shugaban Jami'ar kasa da kasa ta Africa, ya jagoranci taro na Kwamitin Tsarin Mulki na Bankin Afrika a ofishinsa dake cikin Jami`ar.

Wadanda suka halarci zaman, sun hada da  Mataimakin Shugaban Jami'a kan Harkokin kudi da Gudanarwa tare da shugaban kwamotin Dokta Abdo Daoud, yayin da ya tabbatar wa ma halarta irin cigaban da ake samu kuma suka saurari wasu rahotanni masu dacewa daga kwamitocin daban daban kuma ana yin aiki sosai har ma da aikin gine-gine, wanda yakusa kammaluwa nan kusa kadan da yardan Allah.