KUNGIYAR DALIBAN KASAR YEMEN SUN KARRAMA SHUGABAN JAMI'A

    A safiyar jiya lahadi 21/04/2019 mai girma shugaban jami'a Farfesa Kamal Muh'd Ubaid ya gana da shuwagabannin daliban kasar Yemen wa'inda suke karatu a wannan jami'ar ta Afrikiyya. inda daliban suka mikawa shugaban wata kyauta ta musamman don gimamawa agareshi sakamakon hidimtawa al'umma da yakeyi.