ZAMAN FARKO AKAN BATUN ASSASA BANKIN JAMI'A

A ranar Laraba 10/04/2019 a dakin taro na tunawa da Farfesa Attayib dake cikin jami'a aka gudanar da wani zama na musamman wanda ya tattauna dangane da batun kirkiro Bankin jami'a. Zaman ya kankama ne karkashin jagorancin mai girma shugaban jami'a Farfesa Kamal Muh'd Ubaid, da Farfesa Musa Daha ( mataimakin shugaban jami'a a fannin Ilimi da Al'adu), da Dr. Usama Marganiy ( shugaban ofishin zartaswa na jami'a ) da kuma bakin da aka gayata daga wajan jami'a :- Dr. Ibrahim Albulushiy ( shugaban zartaswa na cibiyar Wakafi ) da Dr. Abdou Dawud ( shugaban majalisin assasa Bankuna ) inda suka kammala zaman cikin nasara.

 daga cikin abubuwan da zaman ya fidda :-

                               

  1. Kudin da za'a fara Bankin dasu sai sunkai dalar Amuruka Milayan Dari.
  2. Zaman ya tabbatar da za'a baiwa jami'a kaso 70% don inganta al'amuranta, kaso 30% kuma na habaka kasuwanci.
  3. Za'a karkasa kason jami'ar kamar haka :-

30% da sunan jami'a

10% da sunan ma'akatan jami'a, su kuma ze kasance kamar haka :-

- Matsayin Farfesa zai karbi $500 bayan watanni goma

-Matsayin farfesa na biyu ( Assistant Professor's level ) $400 bayan watanni goma

- Matsayin Dr. zai karbi $300 bayan watannin goma

- Matsayin malami mai karantarwa zai karbi %200 bayan watanni goma

- Kananun ma'akaita daga mataki na 1 zuwa na 3 zasu karbi %100 bayan watanni goma

- Mataki na 4 kuma zai karbi %50 bayan watanni goma

- Karamin ma'aikaci kuma zai karbi %20 bayan watanni goma

15% kuma zai tafi zuwa asoson tsofaffin dalibai

45% kuma za'a barshi ga sauran masana'antu da ma'aikatu

  1. An zabi ginin jami'a mai Lamba 4 da sunan nanne inda zai kasance matabbar Bankin
  2. An zabi shugaban jami'a amatsayin shugaban ofishin majalisar Bankin
  3. An zabi Dr. Abdou amatsayin shugaban Bankin

 Da hakane aka kammala zaman cikin farin ciki da walwala, da kuma fatan Allah Ubangiji ya tabbatar da abubuwan da aka tattauna wanda zasu amfani musulinci da musulmai.