SHAGABAN JAMI'A YA TARBI TAKWARANSA NA JAMI'AR ABDURRAHMAN AS'SAMIT DAKE ZINJIBAR

  A ranar 10/02/2019 mai girma shuagabn jami'a farfesa Kamal Muh'd Ubaid ya karbi bakonci shugaban jami'ar Abdurraman As'samit dake Zinjibari na kasar Tanzaniya. Shugaban tsangayar Doka da Oda ( shari'a ) da na Ilimin addini Musulinci da Mr. Muh'd Abdul ma'aruf ( shugaban ofishin kula da walwalan dalibai ) da Mr. Tajuddin Bashir Niyyam ( shugaban ofishin alakar wajen jami'a ) sun halarci wajen a lokacin zuwan nashi. Mai girma shugaban jami'a yayiwa takwaran nasa tare da 'yan rakiyarsa barka da zuwa, sannan ya basu takaitaccen tarihin wannan jami'a mai albarka. sannan kuma ya tabbatarwa bakon nasa cewa jami'a ashirye take don bada gudun muwa ga jami'ar ta Abdurrahman As'samit.  Anasa bangaren, babban bakon ya yabawa dangane da kyakkywan tarban da suka samu daga jami'ar. sannan ya karfafa batun kulla alaka da jami'ar ta Afrikiyya don inganta harkar Ilimi.