JAMI'A ZATA BUDE KWALEJOJIN KOYON LARABCI A KASASHEN SOMALIYA DA HABASHA ( ITOFIYA )

   A ranar 10/02/2019 mai girma mataimakin shugaban jami'a a fannin ilimi da al'adu Farfesa Musa Daha Tayyallah ya jagoranci wani zama wanda aka gudanar dashi domin bude wasu cibiyoyin koyan harshen Larabci a kasashen Somaliya da kuma Habasha. Zaman ya gudana ne a dakin taro na tunawa da Farfesa Attayib Zainul abideen dake cikin jami'ar. inda zaman ya tattaro : mai girma shugaban jami'a, shugaban tsangayar koyar da Larabci, shugaban tsangayar Horas da malamai,  Farfesa Hasan Makiy ( tsohon shugaban jami'a ) da sauran masu abun cewa acikin lamarin. A farkon al'amarin, Farfesa Musa Daha yayiwa daukacin mahalarta taron barka da zuwa, sannan ya bayyana musu makasudin wannan zaman, ( bude Kwalejojin koyar da Larabci a kasashen Somaliya da Habasa ) domin kara yada harshen a kasashen Afrika. Daukacin mahalarta zaman sun amince da wannan gudirin don kara yada yaren ( Larabci ) ta hanyar da tadace. sannan aka shiga dogon naziri don ganin yadda za'a fuskanci wannan al'amari, inda aka bar al'amarin tsakanin tsangayar koyar da harshen Larabci da kuma jami'o'in Habasan dana Somaliya.  Mai girma shugaban jami'a ya bayyana wannan gudirin a matsayin hanya mafi sauki wajen yada Larabci da kuma bashi kariya.