SHUGABAN JAMI'A YA ZIYARCI MINISTAN KIYON LAFIYA

   A ranar 10/02/2019 mai girma shugaban jami'a Farfesa Kamal Muh'd Ubaid ya ziyarci Ministan kiwon lafiya na babban birnin Khartoum dake nan Sudan. a yayin ziyarar tasa, ya samu rakiyar Farfesa Muh'd Hasan Attakina ( shugaban horaswa na kiwon lafiya ) inda  suka tattauna akan wasu abubuwa masu matukar mahimmanci wanda zasu kara inganta harkar kiwon lafiya a jami'ar ta Afrikiyya. Ministan kiwon lafiyan ya tabbatar masa da cewa ma'aikatarsa zata baiwa jami'ar duk abunda ake bukata  ( dokoki ) don kammala ginin Asibitin da jami'ar take gudanarwa yanzu haka. Sannan kuma aka baiwa daliban jami'ar cigaba da zuwa wasu Asibitoti wanda abaya an dakatar dasu daga zuwa.

  Mai girma shugaban jami'a ya tabbatar da tanadar malaman kiwon lafiya da kuma duk wani abu da yakamata a daukacin cibiyoyin kiwon lafiya wa'inda suke rataye a wuyar jami'ar.