ZAMA NA 35 AKAN TAKARDUN SAKANDIRE

A ranar 06/02/2019 an gudanar da zama akan Takardun Sakandare wanda shugaban jami'a Farfesa Kamal Muh'd Ubaid ya jagoranta. zaman ya gudana ne a dakin taro na tunawa da Farfesa Attayib Zainul'abideen dake cikin jami'ar,  Farfesa Musa Daha Tayyillah ( mataimakin shugaban a fannin Ilimi da Al'adu ) da Dr. Daha Husain ( shugabn Markaz Al'islamiy kuma sakataren kula da Takardun ) da kuma wasu daga cikin wanda abun yake wuyansu ( cikin gida Sudan da wajenta ) duk sun halarci zaman. Zaman dai ya tattauna akan wasu abubuwa wanda zasu zamanantar da Takardun na Sakandire, inda suka tabbatar da Takardun na 2018-2019, sannan kuma aka rattaba hannu akan batun kudi na watan Satumba 2018, har ila yau, an kusanto da wasu abubuwan da zasu maida Takardun na kasashen Afrika su zamo tamkar abu daya.