A safiyar yau Lahadi 04/11/2018 Dr. Musa Daha Tayyallah ( mataimakin shugaban jami'a afannin ilimi ) ya gana da Sakataren Hilal Al-Ahmar na kasar Qatar. Dr. Ayid ( daya daga cikin yan majalisar jami'a ) shine ya jagorancesa zuwa wajen sakataren. Dr. Musa Daha ya tattauna da sakataren, inda yayi masa cikkaken bayani akan abunda yashafi jami'a da irin kokarinta na ilimantar da al'ummar masamman yan Afrika,  sannan kuma ya nuna yardan jami'a dangane da abubuwan da zasu kulla alaka tsakanin bangarorin biyu. Bayan haka , Dr. Musa Daha ya mika masa katin gayyata zuwa taron da jami'a zata gudanar a watan Junairu mai zuwa. Dr. Musa Daha ya gana da Assheikh Yusuf Al'kawariy ( shugaban cibiyar Qatar Al-Khairiya ) inda ya mika masa sakon gaisuwa daga jami'a akan irin gudun muwar da cibiyar take baiwa jami'ar. Mai girma mataimakin shugaban jami'a ya gana da Mr. Muh'd Jabir Al'manaeey ( shugaban ofishin harkokin Addini da Wakafi na kasar Qatar ), inda sukayi alkawarin gina wani yanki daga cikin abubuwan da jami'ar take bukata.