Jiya Asabar 03/11/2018 majalisar ilimi ta gudanar da zama mai lamba ta 140. An gudanar da zaman ne a dakin taro na tunawa da Prof. Attayib Zain Al-Abideen dake cikin jami'ar. Mai girma shugaban jami'a Prof. Kamal Muh'd Ubaid shine wanda ya jagoranci zaman. cikin wa'inda suka halarci zaman akwai Dr. Samir Kurashiy ( wakilin mataimakin shugaban jami'a afannin ilimi ) da Dr. Usama Marganiy Rashid ( mai baiwa shugaba sharawa akan abunda yashafi gudanarwa ) da Dr. Ja'afar Hasan Badiy ( wakilin mataimakin shugaba a fannin  kudi ) da kuma sauran yan majalisar.

 Zaman ya tattauna ne akan abubuwa dawaya mababbanta, da ciki, sun tabbatar da abubuwan da aka tattauna akai a zaman da yagabata, sannan kuma aka bada damar baiwa dalibai sakamakon jarabawansu tun daga matakin Diploma har izuwa sauran matakai. Sannan shugaban ofishin karatun sama da Digri ya bijiro da wani sabon tsari akan masu karatu ta hanyar bincike ( rubutu ). haka kuma yan majalisar sun bada damar fara koyar da harshen Turkiyya a matakin Digri. sannan kuma suka tabbatar da fara Digri na biyu akan abunda yashafi Lissafi (accounting ).