Jiya Laraba 31/10/2018 Dr. Musa Daha Tayallah ( mataimakin shagaban jami'a afannin ilimi ) ya isa kasar Qatar don gudanar da wasu al'amura da suka shafi jami'a. Kai tsaye ya gana da 'yan majalisar dattawan jami'ar dake kasar, karkashin jagorancin daya daga cikinsu kuma shugaban cibiyar Raf  mai suna A'eed Bin Dabsan. sun tattauna akan yadda zuwansu  taron jami'a zai kasance a watan Junairuy mai zuwa, sannan kuma suka tattauna akan wasu abubuwa na daban. Mataimakin shugaban jami'a zeci gaba da ziyarar wurare da ma'aikatu daban daban har zuwa lokacin da zai karkare ziyararsa ya dawo gida.