A safiyar jiya Lahidi 07/10/2018 mai girma  shugaban kwamitin zartaswa na jami'a Dr. Mustafa Usman ya gudanar da wata ziyara domin ganin irirn aikace-aikacen da jami'a take gudanarwa a wannan shekaran. Mai girma shugaban jami'a Prof. Kamal Muh'd Ubaid shine wanda ya jagorance shi izuwa wurare daban daban don ganin aiyukan. daga cikin inda suka ziyarta akwai sabon dakin taro na Prof. Hasan Makkiy da dakunan watsa labarai na Talabijin da Rediyo  da kuma dakunan jarabawa na yanar gizo da dai sauran wuraren da yakamata ya leka.