A safiyar jiya Lahadi da misalin karfe 11:00 na safe, mai girma mataimakin shugaban jami'a a fannin ilimi Dr. Musa Daha Tayyallah ya jagoranci bikin bude taron baje kolin littattafan jami'a wanda wani Kamfanin buga littafai dake Masar tare da hadin gwiwar ofishin kula dakunan karatu na jami'a ( Libraries ) suka hada.   Shugaban kula da dakunan karatu Dr. Abdullah Abdulkhaliq da sauran jagorurin tsangayun jami'ar da wasu ma'abota bincike-bincike na ilimi duk sun samu damar halartan bikin bodewa. Cikin kalamansa Dr. Musa Daha yayi kira ga malamai harda dalibai cewa: sudaure su halarci wannan biki da akeyi tun daga farkonsa har izuwa karshe don samu fa'ida mai girma acikin hakan. ya kara da cewa : irin wannan hadin gwiwa abun alfahari ne ga jami'a harma da dalibanta, sannan yayi godiya ga ofishin kula da dakunan karatu wanda shine ya gayyato wannan Kamfanin.

 Shima anasa bangaren shugaban Kamfanin buga littattafan ya tofa albarkacin bakinsa, inda ya yabi jami'a tare da ofishin kula da dakunan karatu wajan kawo abunda zai ciyar da daliban jami'ar gaba.