A ranar Al-hamis din da tagabata 04/10/2018 mai girma shugaban jami'a tare da jama'arsa suka dunguma daga garin Maiduguri zuwa garin Kaduna dake arewacin kasar Najeriya domin halarta bikin karrama fitaccen dan kasuwan nan wato Alhaji Muh'd Indimi. Bikin karramawan ya biyo bayan irin kokarin da dan kasuwan yakeyi ne na tallafawa gajiyayyo wanda rikicin Boko Haram ya ritsa dasu. An hada bikin karramawan ne tare da bikin yaye wasu dalibai ( sojoji ) da kuma karban wasu sababbin daliban, Alhaji Muh'd Indimi ya gabatar da kalmar godiya ayayin karramasu, sannan kuma wannan makarantar ta NDA ta karrama shugaban jami'a amatsayin babban bako wanda yazu daga wata kasa don taya abokinsa murnan samun wannan matsayi. Mai girma shugaban jami'a gana da jakadan kasar Sudan bayan kammala taron.