Wannan cibiyar mai suna asama ta gudanar da bikin yaye wasu dalibai ( sojoji ) karo na 59 da kuma karbar tawaga ta 60. Bikin yaye daliban ya gudana ne a ranar Laraba 03/10/2018 a dakin taro na Prof. Attayb Zain dake cikin jami'ar. Dr. Ibrahim Khidr ( shugaban tsangayar koyo da koyarwa "education") da shugaban rikon kwarya na jami'a da Dr. Adam Daha Husain ( shugaban cibiyar ) da wakilin rundunan sojojin kasar ta Sudan duk sun halarci bikin. An gabatar da wakoki irin nasu na sojoji da wasu kalamai masu karfafa gwiwa ga sojoji.  Wakilin rundunar sojojin yayi kalamai masu dadi ga wannan cibiya akan gudun muwarta ga hukumar sojojin kasan ta hanyar koyar dasu addinin musulinci. Shima shugaban tsangayar koyo da koyar Dr. Ibrahim Khidr ya jinjinawa hukumar sojojin akan kokarinta na tabbatar da zaman lafiya akasar, da kuma kwadayinta na ganin ta horas da 'ya'yan dai-dai da karantarwan addinin musulinci.  sannan ya kara tabbatar da cigaban wannan al'amari atsakaninsu har illa masha Allahu. daga karshe an mikawa daliban takardun shaidan kammala karatu a wannan cibiya.