Daliban wannan kasar ta Uganda sun sanya wata gasar kwallon kafa atsakanin kasashen Afrika sakamakon murnar zagayowan ranar samun 'yanci ga kasar tasu. Anfara kwallon ne a yammacin jiya Lahadi a babban filin motsa jiki dake cikin jami'ar tsakanin kasar Senegal dasu masu masaukin baki. inda akalla kasashe guda 8 zasu gabza har izuwa lokacin da za'a fidda gwani. Kasashen sune kamar haka : KENYA, MALAWI, MOZAMBIK, GHANA, TCHADI, SENEGAL, TANZANIYA DA KUMA UWAR GAYYA WATO UGANDA.