Cigaba da gudanar da aiyukan hadan gwiwa atsakanin jami'ar Maiduguri dake kasar Najeriya da kuma jami'ar Afrikiyya dake Sudan, wasu malaman jami'ar ta Afrikiyya su biyar (5) daga bangare daban-daban na jami'ar sun isa birnin Maiduguri domin koyan harshen turanci ( rubutu da karatu ) har na tsawon watanni uku.  Shugaban jami'ar Maiduguri shine wanda ya tarbi bakin alokacin zuwansu.