Cikin irin aiyukan da jami’a take gunadarwa don kara fadada harkan ilimi a fadin duniya,  aranar Talatan data gabata ne 07/08/2018 jami’a ta sanya hannu awata takardan yarjejeniya da kulla alaka tsakaninta da jami’ar Imamu Shafi’i dake kasar Somalia. Sanya hannun ya biyo bayan wata ziyara ce wacce mai girman shugaban  ministocin kasar Somalia tare shugaban jami’ar ta Imamu Shafi’I suka kawo nan jami’ar Afrikiyya.

Mai girma shugaban ministocin  kuma daya daga cikin yan majalisar jami’ar ta Imamu Shafi’I yayi godiya ga jami’a kan amincewarta da gudirinsu na kulla alaka da ita amatsayinta na uwa ga ‘yan Afrika masamman ‘yan Somalia.

  Dr. Musa Daha ( mataimakin shugaban jami’a afannin ilimi) shine wanda ya sanya hannu da sunan jami’a. adaya bangaren kuma Dr. Abdulkadir sheikh Isma’il ( shugaban jami’ar ta Imamu Shafi’I ) ya sanya hannu.

Dr. Musa Daha ya gabatar da taswirin gina  gidan Talabijin na jami’ar Imamu Shafi’I din kamar yadda suka nemi gudun muwar jami’a akan haka.