A jiya Latala 07/08/2018  wannan kwalejin maisuna asama ta gudanar da wani bikin yaye dalibanta wa'inda suka kammala karatunsu a wannan shekara ta 2018. Bikin ya gudana ne a dakin taro dake cikin jami'ar, inda manya manya daga masu fada aji na jami'a suka halarci bikin. daga cikin mahalarta bikin akwai Dr. Ibrahim Alkhidr Alhasan ( shugaban kwalejin koyo da kpoyarwa " Education ") wanda shine ya wakilci mataimakin shugaban jami'a afannin ilimi. Har ila yau daga cikinsu akwai Dr. Abdulhay Yusuf ( shugaban kwalejin ) da kuma wasu shuwagabannin kwalejoji da malamai da kuma yan uwa da abokan arziki duk samu damar halartar bikin.

A farkon fara bikin, Dr. Abdulhay Yusuf yayi maraba ga daukacin mahalarta taron, sannan kuma yaja hankalin al'ummah da cewa : wannan  karatu shine asalin kowani irin karatu a duniya gaba daya, kuma shine ilimin da zaka bautawa Allah madaukakin sarki dashi. sannan ya jinjinawa daliban da irin kokarinsu da kuma jajircewar su akan karatunsu. ya kara da cewa kada su manta cewa  su wakilaine ga musulinci da musulmai aduk inda suke. akarshe yayi musu fatan alheri gaba daya.

  Shima babban bako kuma wakilin mataimakin shugaban jami'a awajen bikin wato Dr. Ibrahim Alkhidr Alhasan ya jinjinawa daliban kuma yayi yabo agaresu. sannan kuma yayi kira agare su da sukasance masu kwatanta abunda suka koya daga jami'a. sannan kuma yayi musu fatan alheri tare da cin nasara a duk inda rayuwa takai su.

  Akarshe, kungiyar daliban ta mika kyauta zuwa ga jami'a da kuma shugaban kwalejin tasu. sannan kuma suma aka basu nasu kyauttutukan.