A jiya Litinin 06/08/2018 wannan kwaleji mai suna asama tare da hadin gwiwar ofishin inganta al'amura na jami'a suka shirya wani taro mai taken " Dogaro da Kai" wanda aka gudanar adakin taro dake jami'a. Prof. Muhmud Abdurrahman Assheikh " shugaban ofishin ofishin inganta al'amura na jami'a" kuma wakilin jami'a awajen " da Prof. Amin Al'akibu "wani mai karantar da ilimin kula da lafiyar yara daga jami'ar kimiya da fasaha anan Sudan"  duk sun halarci taron.

 

 A farkon taron Dr. Hindu Ma'amun Buhairiy ( shugabar kwalejin koyar da aikin jinya ) tayi maraba ga daukacin mahalarta taron. sannan kuma tayi magana akan mahimmancin dogaro da kai,  sannan kuma ta mika godiya ta musamman ga Prof. Muhmud Abdurrahman

  Bayan haka Dr. Karimuddin Muh'd Salih yayi magana akan wai shin menene ake nufi da inganci a rayuwa, inda shi kuma Dr. Waliddin Annur yayi sharhi akan bayaninsa. sannan aka rarraba jama'a wurare daban-daban  don aiwatar da abunda aka gudanar a wajan taron.

 Dr. Asma'u Nuridda'im ( shugabar kwalejin koyar da zamantakewar iyali ) da Prof. Azzain Ahmad ( shugaban kwalejin ma'adanai ) da Dr. Kulthum Ibrahim ( shugabar kwalejin koyar da aikin jinya a jami'ar Ribad ) da  Dr. Hafsah Annur da wasu masu fada aji a fannin lafiya daga wasu jami'o'in duk sun halarci taron.

 Akarshe Dr. Hindu Ma'amun tayi godiya ga daukacin mahalarta taron tareda fatan Allah Ubangiji ya maida gidansa lafiya.