A safiyar jiya Laraba 11/07/2018 shugaban jami'ar Baraka  dake birni Abeche na kasar Chadi tare da jama'arsa sun kawo wata ziraya ga jami'ar Afrikyya. Inda mai girma shugaban jami'a Prof. Kamal Muh'd Ubaid ya tarbesu a ofishinsa dake cikin jami'a. Atare da shi akwai Dr. Samir Alqarshiy ( wakilin mataimakin shugaban jami'a a fannin ilimi ) da kuma Mr. Qamar Al'anbiya Isa ( shugaban ofishin hadaka da labarai).

Mai girma shugaba yayiwa takwaran nasa barka da zuwa, inda wakilin mataimakin shugaban ya tabbatar da shirin jami'a na karbar kudirinsu akan abunda ya shafi hadin gwiwa da taimakekeniya atsakaninsu. 

Anashi bangaren, shugaban jami'ar ta Baraka yayi sharhi ne akan jami'ar tasa. inda ya bayyana cewa : jami'ar tasu tana bukatan gudun muwa ta kowani fanni daga jami'ar ta Afrikiyya, kasancewar jami'ar tasu jaririya ce mai dauke da kwalejoji guda hudu ( 4 ).

Mai girma shugaba ya kara jaddada maraba da takwaransa akan wannan ziyara tashi da kuma kwadayin sa na kulla akala da jami;ar ta Afrikyya. mai girma shugaban ya kara tabbatarwa abokin nasa cewa jami'a zata tsaya tsayin daka don bada gudun muwar ga jami'ar ta Baraka a duk lokacin da bukatar hakan yazo. sannan kuma mai girma shugaba yabasu wasu shawarwari da zasu amfanesu don jami'ar tasu tasamu daukaka.