Cikin irin kokarin da jami'a takeyi na zamanantar da tsarin karatu, a jiya Laraba 11/07/2018 wakilin jami'a a taron jami'i'o'in Asia wanda ya gudana a birnin Surabaya dake kasar Indonusia ya sanya hannu tsakanin jami'a da wasu jami'o'i.

  Sanya hannu ya fara da jami'ar Sydney dake Australia, jami'ar Hindustan dake Indiya, da kuma jami'ar Georgia. inda suka tabbatar da hadin gwiwa da taimakekeniya a fannin ilimi da bincike-bincike da sauransu.  Irin wannan al'amari dai zai karawa jami'a kima da daukaka a idon duniya.    Wakilin jami'a Dr. Musa Daha ( mataimakin shugaban jami'a a fannin ilimi da aiyukan cigaba ) ya bayyana matsayin jami'ar ta Afrikiyya ta hanyar basu cikakken sharhi akan jami'ar.

 A yau Alhamis ne akesa rai wakilin jami'ar zai dawo bayan ya kwashe wasu kwanaki yana hidima ga jami'a.