A jiya Talata 10/07/2018 jami'a ta karbi wasu baki wa'inda suka kawo ziyara ta musamman daga kwalejin sadarwa dake garin Jazeera. Sun kawo ziyarar ne a sakamakon wani shirinsu na abokantaka na harkar labarai wanda kwalejin ta shirya tare da hadin gwiwar wata jami'a dake koyar da aikin sadarwa dake cikin garin Sudan. Dr. Salwa Hasan ( Director of the Sudan Academy of Communication Sciences ) itace ta jagoranci bakin. Dr. Assafir Khadr Harun ( shugaban kwalejin sadarwa ) shine wanda ya tarbe su daidai lokacin da Prof. Badr deen Ahmad Ibrahim ( malami a kwalejin ) da Mr. Mu'utasim Fadil ( shugaban gidan Rediyon Afrikiyya ) da Mr. Hateem Babikr ( shugaban gidan Talabijin na Al'alamiyya )  suka halarci tarban bakin.

Dr. Khidr Harun ( shugaban kwalejin sadarwa ) yayi musu barka da zuwa. sannan suka fara tattaunawa cikin al'amuran da zasu kawo cigaba da habaka wannan fanni na sadarwa kasancewar sadarwa abune mai matukar mahimmanci a wannan zamani da muke ciki. Bayan kammala tattaunawar su, bakin sun kewaya cikin kwalejin ta sadarwa sannan daga baya sukaci abinci  tare da sauran ma'aikata.