A ranar Talata 15/05/2018 aka kulle taron  bikin horaswa karo na biyu wannan jami'a da masu kula da wannan fannin suka shirya karkashin jagorancin Mr. Anas Mahdiy Annazir ( mai kula da abubuwan da suka shafi fasaha ) da Dr. Sara Muh;d Aliy ( shugabar shashun fasaha ) da Dr.  Khalid  Muh'd Anaan ( shugaban "laborataries" ) inda aka horas da malamai sama da 15 daga kwalejojin kimiya da fasaha daban-daban akan wannan bangaren ( DNA, PCR, GEL, ELECTROPHORSIS ) aranar karshe, malaman da aka horas sun fara gudanar da abunda suka koya kai tsaye, sannan suka nuna jin dadinsu, inda sukayi fatan jami'a ta kara shirya musu irin wannan horaswa zuwa gaba.  Karshe sunyi godiya ga uba kuma jagora na gari wato mai girma shugaban jami'a prof. Kamal Muh'd Ubaid dayasamu damar halartar bikin nasu.