A ranar Talatar da tagabata 15/05/2018 wannan kwalejin mai suna asama ta karbi wasu baki wa'inda suka fito daga kasar  Turkiyya karkashin jagorancin shugaban cibiyar Attau'iyya Attarkiya wacce take aikinta anan kasar Sudan. Dr. Ahmad Attahir ( mataimakin shugaban ofishin magudanar albarkatu ) da Dr. Abdulfatah Bilal ( shugaban kwalejin Injiniyanci ) suka tarbi bakin alokacin da suka iso jami'ar. Bakin dai sun saurari bayanai daban-daban dangane da kwalejin dama jami'ar kanta.