A ranar Lahadin da tagabata ne 15/04/2018 mataimakin shugaban jami'a a fannin ilimi da aiyukan cigaba Dr. Musa Daha Tayyillah ya karbi bakuncin wasu baki mata daga majalisar kungiyoyin Afrika. an tarbe bakin ne a ofishin jami'a, inda shugabar kwalejin koyar da aikin jinya Dr. Hindu Ma'amun Buhairiy da Dr. Taj Adeen Bashir Niyam ( shugaban ofinshin harkokin wajen jami'a ) da Dr. Azhariy Attijaniy Iwad ( daya daga cikin 'yan kungiyar ) duk suka halarci wajan.

Da farko dai mai girma mataimakin shugaba yayima bakin nasu barka da zuwa, sannan yayi musu cikakken bayani dangane da jami'a da abunda jami'ar ta kunsa tun daga dalibanta da kwalejojinta dama yanayin gudanar da aiyukanta. sannan yace jami'a ashirye take don kulla alaka da kungiyar tasu don tabbatar da kowani irin cigaba ga al'umma.

Ita kuwa shugabar bakin Ms Ana Mugabi tayi godiyane kan irin karamcin da suka samu awajan jami'a, sannan ta jinjinawa jami'ar kan irin yadda take taka rawar gani na abunda yashafi ilmi a Afrika dama duniya baki daya.

sannan ta tabbabtar da kula alaka tsakanin kungiyar tasu da jami'a. bayan haka, anyi fira kai tsaye da Ms Ana a gidan talabijin na Al'alamiyya mallakar jami'ar, inda firar ta gudana cikin harshen turanci.