Cikin ikion ALLAH anfara gudanar da aiki a sabon gidan gonar jami'a mai fadin mita 3000  dake Umdurman. Aikin wanda kamfanin Wailaz ya amshi kwangilarshi a hannun jami'a, inda ayanzu haka suke gudanar da aikinsu cikin annashuwa da nishadi, sundai fara fidda hanyoyin ruwa, sannan kuma zasu tona rijiyoyi daga baya. Mai girma shugaban jami'a da jama'arshi sun kai ziyara wajen da ake gudanar da aikin a ranar 14/04/2018 .

Mai girma shugaban jami'a tare da jama'arshi sunkai ziyara a garin Al'kababish dake kusa da   gidan gonar.

Yana daga cikin aiyukan jami'a kula da al'umma!  Mai girma shugaba da jama'arshi sun samu damar ziyarar cikin kauyen na Al'kababish, inda suka ziyarci makarantu da masallatai, mai girma shugaba yace : jami'a zata cigaba da kula da  makarantu da masallatan kauyen, sannan yace za'a gina musu cibiyar cigaban al'umma a garin nasu, sannan za'a fara turo musu tawagar Da'awa da jami'a take shiryawa lokaci bayan lokaci.

Al'umman wannan kauye dai suna cike da farin ciki na zuwan wannan alheri adai-dai lokacin da suke bukatar haka.