A ranar Alhamis din da tagabata 12/04/2018 mai girma shugaban jami'a prof. Kamal Muh'd Ubaid ya tarbi wasu baki daga kasar Najeriya karkashin jagorancin tsohon shugaban jami'ar Bayaro ( B,U,K ) prof. Muh'd Sani Zahraddin. 

Mai girma shugaban jami'a yayima bakin nasu barka da zuwa kamar yadda aka saba,  sannan yayi musu cikakken bayani dangane da jami'ar ta AFRIKIYYA tun daga adanin dalibanta da yawan kwalejojinta da kuma yanayin gudanar da karatuttukansu da irin gudun muwar da tsofaffin daliban jami'ar suke badawa. sannan ya bayyana musu irin jin dadin da jami'a keyi sakamakon  gudun muwa wanda Muhammadu Indimi yake baiwa jami'ar, wanda shima yana daya daga cikin 'yan majalisar jami'ar. ya kara da cewa : yanzu haka akwai kwaleji guda wacce shi Alhaji Muhammadu Indimin ya ginama jami'a ( kwalejin ma'adanai ), sannan ya dauki nauyin karatun wasu dalibai 'yan Najeriya.

 Jagoran wa'innan baki prof. Muh'd Sani, yaji dadin wannan bayanai da yaji daga bakin mai girma shugaban jami'a, sannan  yayi godiya kan irin yadda aka tarbesu cikin mutuntawa da karramawa. prof. Muh'd Sani ya jinjinawa jami'ar wajen yada ilimi da koyar da 'ya'yayenta  'yan Afrika. Akarshe bakin sun sama damar lekawa wasu daga cikin kwalejojin jami'a harda dakunan yada labarai na jami'ar.

Makasudin zuwan bakin dai shine : halartar wani taro na tunawa da Assheikh Ibrahim Attayb. taron wanda ya gudana a yammacin wannan rana.