A safiyar ranar Al'hamis din da tagabata ne wa'innan ofishoshi masu suna asama suka shirya wani taro kan yadda za'a kawo wani sabon tsari dangane da abunda yashafi harkar bincike na ilimi wato ( research ). Taron wanda ya gudana a dakin taro na Umar Assammaniy karkashin jagorancin mai girma shugaban jami'a prof. Kamal Muh'd Ubaid da kuma wasu daga cikin shuwagabannin kwalejojin jami'ar da kuma wa'inda hakkin kula da binciken ya rataya a wuyansu, da kuma dalibai masu karatun gaba da Digiri. taken wannan taro shine : ( fadakar da masu bincike don tabbatar da ingancin abunda suke bincike akai ).

A karkashin wannan maudu'i, an tattauna akan wasu al'amura masu yawan gaske, wanda zasu tabbatar da abunda ake bukata acikin al'amuran binciken nasu. a cikin maganar da Mr. Mustafa Al'halnakiy ( daya daga cikin ma'aikatan ofishin inganta al'amura ) yayi, yayi magana ne kan yanayin gudanar da bincinke da mafi yawancin jami'o'i suke tafiya akai, sannan ya kara da cewa : lallai bincike na ilimi yana bada gudun muwa mai girma dangane da rayuwar al'ummah, sannan ya karkare kalamanshi da wasu shawarwari da kuma mafita kan al'amarin.

Shi kuwa mai girma shugaban jami'a yayi magana ne akan abu mafi mahimmanci wato dai-daita dabi'un dalibai, sannan yaja hankalin malaman jami'a cewa : yanada matukar mahimmanci da su dinga watsa rubuce-rubucensu acikin yanar gizo mallakar jami'ar, don al'umma sukaru da irin fikirar da Allah ya basu.