Wani dalibi wanda ya fito daga kasar Murtaniya me suna Mahfuz Ahmad Mahfuz Muh'd ya kirkiro wata na'ura da ake iya cire hakori da ita. dalibin wanda ya kammala karatunshi a kwalejin koyan aikin likitanci a jami'ar ta Afrkiyya ( fannin  hakori ). Wannan na'ura ana amfani da ita wajan cire karyayyan hakori, inda dalibin ya sama takardan yabo waccce ta fito daga ma'aikatan Adaci ta Sudan. Ana iya cire hakori da wannan na'ura cikin kankanin lokaci batare da jin zafi ba.

Ansanyama na'uran suna kamar haka ( Abaat Li'izaalati'aljuzoor Al'mutabakkiya ), na'uran tayi kama da silinda ( cylindrical )  tanada tsawon 10 cm.

Wannan dalibi dai yanzu haka yana ma'aikatan kiwon lafiya na kasar ta Sudan inda zeyi wata jarabaawa akan ciwukan da suka shafi fuska da hannaye.